‏ Psalms 129

Waƙar haurawa.

1Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,
bari Isra’ila yă ce,
2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,
amma ba su yi nasara a kaina ba.
3Manoma sun nome bayana
suka yi kunyoyinsu da tsayi.
4Amma Ubangiji mai adalci ne;
ya’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona
a juye da su baya da kunya.
6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi,
wadda takan bushe kafin tă yi girma;
7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa,
balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
8Kada masu wuce su ce,
“Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku;
muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”
Copyright information for HauSRK