‏ Psalms 130

Waƙar haurawa.

1Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
2Ya Ubangiji, ka ji muryata.
Bari kunnuwanka su saurara
ga kukata ta neman jinƙai.

3In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,
Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
4Amma tare da kai akwai gafartawa,
saboda haka ake tsoronka.

5Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
6Raina na jiran Ubangiji
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

7Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
8Shi kansa zai fanshi Isra’ila
daga dukan zunubansu.
Copyright information for HauSRK