Psalms 131
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. 1Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,idanuna ba sa fariya;
ban dami kaina da manyan al’amura ba
ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
2Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;
kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,
kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
3Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji
yanzu da har abada kuma.
Copyright information for
HauSRK