‏ Psalms 132

Waƙar haurawa.

1Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda
da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.

2Ya yi rantsuwa ga Ubangiji
ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
3“Ba zan shiga gidana
ko in kwanta a gado ba,
4ba zan ba wa idanuna barci ba,
ba gyangyaɗi wa idanuna,
5sai na sami wuri wa Ubangiji,
mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”

6Mun ji haka a Efrata,
muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,
Wato, Kiriyat Yeyarim
,
,
Ko kuwa mun ji game da shi a Efrata, mun same shi a filayen Ya’ar. (Kuma babu alamar keɓewa kewaye da ayoyi 7-9)

7“Bari mu tafi wurin zamansa;
bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
8ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka,
kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
9Bari a suturta firistocinka da adalci;
bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”

10Saboda Dawuda bawanka,
kada ka ƙi shafaffenka.

11 Ubangiji ya rantse wa Dawuda
tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa,
“Ɗaya daga cikin zuriyarka
zan sa a kan kursiyinka,
12in’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari
da farillan da na koya musu,
to’ya’yansu maza za su zauna
a kan kursiyinka har abada abadin.”

13Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona,
ya so ta zama mazauninsa,
14“Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin;
a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
15zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa;
matalautanta za su ƙoshi da abinci.
16Zan suturta firistocinta da ceto,
tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.

17“A nan zan sa ƙaho
Ƙaho a nan yana nufin wani mai ƙarfi, wato, sarki.
ya yi girma wa Dawuda
in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
18Zan suturta abokan gābansa da kunya,
amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”
Copyright information for HauSRK