Psalms 133
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. 1Abu mai kyau ne, mai daɗi kumasa’ad da’yan’uwa suna zaman lafiya!
2Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,
yana gangarawa a gemu,
yana gangarawa a gemun Haruna,
har zuwa wuyan rigunansa.
3Yana kamar raɓar Hermon
da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.
Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,
har ma rai na har abada.
Copyright information for
HauSRK