‏ Psalms 134

Waƙar haurawa.

1Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji
waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.
2Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki
ku kuma yabi Ubangiji.

3Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa,
ya albarkace ku daga Sihiyona.
Copyright information for HauSRK