Psalms 135
1Yabi Ubangiji. ▼▼Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a ayoyi 3 da 21.
Yabi sunan Ubangiji;
yabe shi, ku bayin Ubangiji,
2ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji,
cikin filayen gidan Allahnmu.
3Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne;
rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
4Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa,
Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
5Na san cewa Ubangiji yana da girma,
cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.
6 Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,
a sammai da kuma a duniya,
cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
7Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya;
yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama
ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
8Ya kashe’ya’yan fari na Masar,
’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.
9Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar,
a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.
10Ya bugi al’ummai masu yawa
ya kuma karkashe manyan sarakuna,
11Sihon sarkin Amoriyawa,
Og sarkin Bashan
da kuma dukan sarakunan Kan’ana,
12ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo,
abin gādo ga mutanensa Isra’ila.
13Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada,
sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.
14Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi
ya kuma ji tausayin bayinsa.
15Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya,
da hannuwan mutane suka yi.
16Suna da bakuna, amma ba sa magana,
idanu, amma ba sa gani;
17suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
ba kuwa numfashi a bakunansu.
18Waɗanda suka yi su za su zama kamar su,
haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.
19Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji;
Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;
20Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji;
ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
21Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona,
gare shi wanda yake zama a Urushalima.
Yabi Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK