Psalms 137
1A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kukasa’ad da muka tuna da Sihiyona.
2A can a kan rassan itatuwa
muka rataye garayunmu,
3gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,
masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;
suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji
a baƙuwar ƙasa?
5In na manta da ke, ya Urushalima,
bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
6Bari harshena yă manne wa rufin bakina
in ban tuna da ke ba,
in ban so Urushalima
farin cikin mafi girma ba.
7Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi
a ranar da Urushalima ta fāɗi.
Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta,
A ragargaza ta har tushenta!”
8Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,
mai farin ciki ne wanda ya sāka miki
saboda abin da kika yi mana,
9shi da ya ƙwace jariranki
ya fyaɗa su a kan duwatsu.
Copyright information for
HauSRK