‏ Psalms 139

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

1Ya Ubangiji, ka bincike ni
ka kuwa san ni.
2Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi;
ka san tunanina daga nesa.
3Ka san fitata da kuma kwanciyata;
ka saba da dukan hanyoyina.
4Kafin in yi magana da harshena
ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
5Ka kewaye ni, gaba da baya;
ka sa hannunka a kaina.
6Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana,
ya fi ƙarfi in gane.

7Ina zan tafi daga Ruhunka?
Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8In na haura zuwa sammai, kana a can;
in na yi gado a zurfafa, kana a can.
9In na tashi a fikafikan safiya,
in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10can ma hannunka zai bishe ni,
hannunka na dama zai riƙe ni gam.
11In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni
haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”
12duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba;
dare zai haskaka kamar rana,
gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

13Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
15Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
16Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
17Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah!
Yawansu ba su da iyaka!
18A ce zan iya ƙirgansu,
za su fi yashin teku yawa.
Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

19Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah!
Ku rabu da ni, ku masu kisankai!
20Suna magana game da kai da mugun nufi;
maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.
21Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji,
ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?
22Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai;
na ɗauke su abokan gābana.
23Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata;
ka gwada ni ka kuma san damuwata.
24Duba ko akwai wani laifi a cikina,
ka bishe ni a madawwamiyar hanya.
Copyright information for HauSRK