Psalms 143
Zabura ta Dawuda. 1Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,ka saurari kukata don neman jinƙai;
cikin amincinka da adalcinka
ka amsa mini.
2Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,
gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
3Abokin gāba yana fafarata,
ya murƙushe ni har ƙasa;
ya sa ina zama a cikin duhu
kamar waɗanda suka mutu tun tuni.
4Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina
zuciyata ta damu ƙwarai.
5Na tuna da kwanakin baya
na yi tunani a kan dukan ayyukanka
na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
6Na buɗe hannuwana gare ka;
raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela
7Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji;
ƙarfina ya ƙare.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni
in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
8Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,
gama na sa zuciyata a gare ka.
Ka nuna mini hanyar da zan bi,
gama a gare ka na miƙa raina.
9Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,
gama na ɓoye kaina a gare ka.
10Ka koya mini in yi nufinka,
gama kai ne Allahna;
bari nagarin Ruhunka
yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
11Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;
a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
12A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana;
ka hallaka dukan maƙiyana,
gama ni bawanka ne.
Copyright information for
HauSRK