Psalms 148
1Yabi Ubangiji. ▼▼Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 14.
Yabi Ubangiji daga sammai,
yabe shi a bisa sammai.
2Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,
yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
3Yabe shi, rana da wata,
yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
4Yabe shi, ku bisa sammai
da kuma ku ruwan bisa sarari.
5Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama ya umarta aka kuwa halicce su.
6Ya sa su a wurarensu har abada abadin;
ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
7Yabi Ubangiji daga duniya,
ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
8walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,
hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
9ku duwatsu da dukan tuddai,
itatuwa masu’ya’ya da dukan al’ul,
10namun jeji da dukan dabbobin gida,
ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
11sarakunan duniya da dukan al’ummai,
ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
12samari da’yan mata,
tsofaffi da yara.
13Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;
darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
14Ya tayar wa mutanensa ƙaho, ▼
▼Ƙaho a nan na nuna wani mai ƙarfi, wato, sarki.
yabon dukan tsarkakansa,
na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.
Yabi Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK