‏ Psalms 15

Zabura ta Dawuda.

1Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?
Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

2Sai wanda ba shi da laifi
kuma yana yin abin da yake daidai,
wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,
wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta
ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
4wanda yake ƙin mugun mutum
amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,
yakan cika alkawarinsa
ko da ma ya zafe shi,
5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba
kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.

Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa
ba zai taɓa jijjiguwa ba.
Copyright information for HauSRK