‏ Psalms 150

1Yabi Ubangiji.
Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 6.

Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;
yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
3Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
4yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.
Copyright information for HauSRK