‏ Psalms 16

Miktam ne
Kan magana, mai yiwuwa wata kalma ta kiɗa ce.
na Dawuda.

1Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.

2Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;
in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”
3Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa,
su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.
4Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli.
Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba
ko in ambaci sunayensu da bakina.

5 Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;
ka kiyaye rabona,
6Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;
tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.
7Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;
ko da dare ma zuciyata kan koya mini.
8Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

9Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
11Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
Copyright information for HauSRK