Psalms 19
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. 1Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
3Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
4Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
7Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
takan wartsakar da rai.
Farillan Ubangiji abin dogara ne,
suna mai da hikima da sauƙi.
8Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.
9Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,
zai kasance har abada.
Farillan Ubangiji tabbatattu ne,
kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
10Sun fi zinariya daraja,
fiye da zalla zinariya nesa;
sun fi zuma zaƙi
fiye da zuma daga kaki.
11Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;
a kiyaye su akwai lada mai girma.
12Wane ne zai iya rabe kurakuransa?
Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
13Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci;
kada ka bari su yi mulki a kaina.
Ta haka zan zama marar laifi;
marar laifi na babban tawaye.
14Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata
su zama abin gamsuwa a gabanka,
Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.
Copyright information for
HauSRK