Psalms 23
Zabura ta Dawuda. 1Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,2Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa, ▼
▼Ko kuwa ta kwarin mafi duhu duka
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
5Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
6Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
Copyright information for
HauSRK