Psalms 24
Zabura ta Dawuda. 1Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
2gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
3Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?
Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
4Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,
wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki
ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
5Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
6Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan,
waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela
7Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
8Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,
Ubangiji mai girma a yaƙi.
9Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi;
ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi,
don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
10Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji Maɗaukaki,
shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela
Copyright information for
HauSRK