Psalms 25
Ta Dawuda. 1A gare ka Ya Ubangiji,na miƙa raina.
2A gare ka na dogara, ya Allahna.
Kada ka bari in sha kunya,
ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
3Ba wanda yake sa bege a gare ka
da zai taɓa shan kunya,
amma za su sha kunya
su da suke tayarwa babu dalili.
4Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,
ka koya mini hanyoyinka;
5ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,
gama kai ne Allah Mai cetona,
kuma begena yana a kanka dukan yini.
6Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,
gama suna nan tun dā.
7Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata
da kuma hanyoyin tawayena;
bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,
gama kai nagari ne, ya Ubangiji.
8 Ubangiji nagari da mai adalci ne;
saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.
9Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai
ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
10Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci
ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.
11Saboda sunanka, ya Ubangiji,
ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.
12To wane ne mai tsoron Ubangiji?
Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
13Zai ci kwanakinsa a wadace,
kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa;
yakan sa su san alkawarinsa.
15Idanuna kullum suna a kan Ubangiji,
gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
16Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
gama na kaɗaice ina kuma wahala.
17Damuwoyin zuciyata sun ninka;
ka’yantar da ni daga wahalata.
18Ka dubi wahalata da kuma azabata
ka ɗauke mini dukan zunubaina.
19Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru
da kuma yadda suka ƙara ƙina!
20Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
21Bari mutunci da adalci su tsare ni,
domin begena yana a kanka.
22Ka fanshi Isra’ila, ya Allah,
daga dukan wahalarsu!
Copyright information for
HauSRK