‏ Psalms 26

Ta Dawuda.

1Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,
gama na yi rayuwa marar zargi;
Na dogara ga Ubangiji
ba tare da kaucewa ba.
2Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,
ka bincike zuciyata da tunanina;
3gama ƙaunarka kullum tana a gabana,
kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

4Ba na zama tare da masu ruɗu,
ko in yi tarayya da masu riya;
5na ƙi jinin taron masu aikata mugunta
na ƙi in zauna tare da mugaye.
6Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,
ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
7ina shelar yabonka da ƙarfi
ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.

8Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,
wurin da ɗaukakarka ke zaune.
9Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi
raina tare da masu son yin kisankai
10waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,
waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
11Amma na yi rayuwa marar zargi;
ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.

12Ƙafafuna suna tsaye daram;
cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.
Copyright information for HauSRK