‏ Psalms 28

Ta Dawuda.

1A gare ka nake kira,
ya Ubangiji Dutsena;
kada ka yi mini kunnen ƙashi.
Gama in ka yi shiru,
zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.
2Ka ji kukata ta neman jinƙai
yayinda nake kira ka don neman taimako,
yayinda nake daga hannuwana
wajen Wurinka Mafi Tsarki.

3Kada ka ja ni tare da mugaye,
tare da masu yin mugunta,
masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu
amma suna riƙe da su a zukatansu.
4Ka sāka musu da ayyukansu
da kuma don mugun aikinsu;
ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi
ka kuma mayar musu abin da ya dace da su.

5Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji
da abin da hannuwansa suka yi ba,
zai rushe su
ba kuwa zai ƙara gina su ba.

6Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

8 Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa,
kagarar ceto domin shafaffensa.
9Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka;
ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.
Copyright information for HauSRK