Psalms 29
Zabura ta Dawuda. 1Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
2Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
3Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,
Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.
4Muryar Ubangiji mai iko ce;
muryar Ubangiji da girma take.
5Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.
Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
6Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,
Siriyon ▼
▼Wato, Dutsen Hermon
kuma kamar ɗan jakin jeji.7Muryar Ubangiji ta buga
da walƙatar walƙiya.
8Muryar Ubangiji ta girgiza hamada
Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.
9Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ▼
▼Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu.
ya kakkaɓe itatuwan kurmi.
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;
Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.
Copyright information for
HauSRK