Psalms 30
Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. ▼▼Kan magana, ko kuwa faɗa
Ta Dawuda. 1Zan girmama ka Ya Ubangiji,gama ka tsamo ni daga zurfafa
ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
2Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako
ka kuwa warkar da ni.
3Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;
ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
4Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
5Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
6Sa’ad da nake lafiya, na ce,
“Ba zan jijjigu ba.”
7Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri,
ka sa katangar dutsena ya tsaya daram;
amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka,
sai in cika da tsoro.
8A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira;
a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.
9“Wace riba ce a hallakata,
a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami?
Ƙura za tă yabe ka ne?
Za tă iya yin shelar amincinka?
10Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai;
Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”
11Ka mai da kukata ta zama rawa;
ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
12don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba.
Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.
Copyright information for
HauSRK