‏ Psalms 32

Ta Dawuda. Maskil
Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.
ne.

1Mai farin ciki ne shi
wanda aka gafarta masa laifofinsa,
wanda aka shafe zunubansa.
2Mai farin ciki ne mutumin
da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa
wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.

3Sa’ad da na yi shiru,
ƙasusuwana sun yi ta mutuwa
cikin nishina dukan yini.
4Gama dare da rana
hannunka yana da nauyi a kaina;
an shanye ƙarfina ƙaf
sai ka ce a zafin bazara. Sela

5Sa’an nan na furta zunubina a gare ka
ban kuwa ɓoye laifina ba.
Na ce, “Zan furta
laifofina ga Ubangiji.”
Ka kuwa gafarta
laifin zunubina. Sela

6Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka
yayinda kake samuwa;
tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,
ba za su kai wurinsa ba.
7Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela

8Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;
Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
9Kada ka zama kamar doki ko doki,
wanda ba su da azanci
wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama
in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
10Azaban mugu da yawa suke,
amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa
kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

11Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;
ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!
Copyright information for HauSRK