Psalms 33
1Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ▼
▼Ko kuwa teku sai ka ce a tsibi
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai;
yakan wofintar da manufofin mutane.
11Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,
manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
12Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta,
mutanen da ya zaɓa don gādonsa.
13Daga sama Ubangiji ya duba
ya kuwa ga dukan’yan adam;
14daga mazauninsa yana lura
da dukan waɗanda suke zama a duniya,
15shi da ya yi zukatan duka,
wanda yake kula da kome da suke yi.
16Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa;
ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
17Dogara a kan doki don ceto banza ne;
duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
18Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
20Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
21A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
22Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
Copyright information for
HauSRK