Psalms 36
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. 1Akwai magana a cikin zuciyatagame da zunubin mugu.
Babu tsoron Allah
a idanunsa.
2Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne
wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
3Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu;
ya daina zama mai hikima da yin alheri.
4Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta;
yakan sa kansa ga aikata zunubi
kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.
5Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai,
amincinka har sararin sammai.
6Adalcinka yana kama da manyan duwatsu,
hukuncinka kamar zurfi mai girma.
Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.
7Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!
Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.
8Suna biki a yalwar gidanka;
kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.
9Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai
cikin haskenka mukan ga haske.
10Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka,
adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.
11Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini,
ko hannun mugu ya kore ni.
12Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi,
a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!
Copyright information for
HauSRK