‏ Psalms 38

Zabura ta Dawuda. Roƙo ne.

1Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
ko ka hore ni cikin hasalarka.
2Gama kibiyoyinka sun soke ni,
hannunka kuma ya fāɗo a kaina.
3Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;
ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
4Laifofina sun mamaye ni
kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.

5Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari
saboda wawancina na zunubi.
6An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni;
dukan yini ina ta kuka.
7Bayana yana fama da zazzaɓi;
babu lafiya a jikina.
8Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni;
ina nishi da wahala a cikin zuciyata.

9Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji;
ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
10Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare,
har ma haske ya rabu da idanuna.
11Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna;
maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
12Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu,
waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni;
yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

13Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji,
kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa.
14Na zama kamar mutumin da ba ya ji,
wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa.
15Na dogara gare ka, ya Ubangiji;
za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.
16Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina
ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”

17Gama ina gab da fāɗuwa,
kuma cikin azaba nake kullum.
18Na furta laifina;
na damu da zunubina.
19Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi;
waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.
20Waɗanda suke sāka alherina da mugunta,
suna cin zarafina
sa’ad da nake bin abin da yake daidai.

21Ya Ubangiji, kada ka yashe ni;
kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.
22Zo da sauri ka taimake ni,
Ya Ubangiji Mai Cetona.
Copyright information for HauSRK