Psalms 4
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. 1Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka,Ya Allahna mai adalci.
Ka ba ni sauƙi daga wahalata;
ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.
2Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?
Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela
3Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa;
Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.
4Cikin fushinku kada ku yi zunubi;
sa’ad da kuke kan gadajenku,
ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela
5Ku miƙa hadayun da suka dace
ku kuma dogara ga Ubangiji.
6Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
7Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
8Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
Copyright information for
HauSRK