Psalms 41
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. 1Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa
ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
4Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai;
ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
5Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa,
“Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
6Duk sa’ad da wani ya zo ganina,
yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;
sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
7Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;
suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
8“Mugun ciwo ya kama shi;
ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
9Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
10Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,
ka tā da ni, don in sāka musu.
11Na sani kana jin daɗina,
gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
12Cikin mutuncina ka riƙe ni
ka sa ni a gabanka har abada.
13Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
har abada abadin.
Amin kuma Amin.
Copyright information for
HauSRK