Psalms 43
1Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah,ka kuma nemi hakkina
a kan al’ummai marasa sanin Allah.
Ka kuɓutar da ni daga
masu ruɗu da mugayen mutane.
2Kai ne Allah mafakata.
Me ya sa ka ƙi ni?
Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,
a danne a hannun abokin gāba?
3Ka aiko da haskenka da gaskiyarka,
bari su bishe ni
bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki,
zuwa wurin da kake zama.
4Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,
ga Allah, farin cikina da murnata.
Zan yabe ka da garaya,
Ya Allah, Allahna.
5Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?
Me ya sa ka damu a cikina?
Ka dogara ga Allah,
gama zai sāke yabe shi,
Mai Cetona da Allahna.
Copyright information for
HauSRK