‏ Psalms 44

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’ya’yan Kora maza. Maskil
Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
ne.

1Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah;
kakanninmu sun faɗa mana
abin da ka aikata a kwanakinsu,
tun dā can.
2Da hannunka ka kori al’ummai
ka kuma dasa kakanninmu;
ka ragargaza mutanen
ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.
3Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar,
ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba;
hannun damanka ne, ƙarfin hannunka,
da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.

4Kai ne Sarkina da kuma Allahna,
wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
5Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya;
ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.
6Ba na dogara ga bakana,
takobina ba ya kawo nasara;
7amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,
ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.
8A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini,
kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela

9Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu;
ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
10Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba,
kuma abokan gābanmu suka washe mu.
11Ka ba da mu a cinye kamar tumaki
ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.
12Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba
babu wata riba daga sayar da su da ka yi.

13Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu,
abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
14Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai;
mutanen suna kaɗa mana kai.
15Dukan yini ina cikin wulaƙanci,
fuskata kuma ta rufu da kunya
16saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina,
saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

17Dukan wannan ya faru da mu,
ko da yake ba mu manta da kai ba
ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
18Zukatanmu ba su juya baya;
ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
19Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji
ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.

20Da a ce mun manta da sunan Allahnmu
ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
21da Allah bai gane ba,
da yake ya san asiran zuciya?
22Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini;
aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.

23Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci?
Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.
24Me ya sa ka ɓoye fuskarka
ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?

25An kai mu ƙasa zuwa ƙura;
jikunanmu sun manne da ƙasa.
26Ka tashi ka taimake mu;
ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.
Copyright information for HauSRK