Psalms 47
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. 1Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai;ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.
2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne,
Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
3Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu,
mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.
4Ya zaɓar mana gādonmu,
abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela
5Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki,
Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.
6Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;
ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
7Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;
ku rera zabura ta yabo gare shi.
8Allah yana mulki a bisa al’ummai;
Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.
9Manyan mutanen al’ummai sun taru
a matsayin mutanen Allah na Ibrahim,
gama sarkunan duniya na Allah ne;
ana ɗaukaka shi ƙwarai.
Copyright information for
HauSRK