‏ Psalms 50

Zabura ta Asaf.

1Maɗaukaki, Allah, Ubangiji,
ya yi magana ya kuma kira duniya
daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.
2Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau,
Allah na haskakawa.
3Allahnmu yana zuwa
ba kuwa zai yi shiru ba;
wuta mai cinyewa a gabansa,
babban hadari kuma ya kewaye shi.
4Ya kira sammai da suke bisa,
da duniya, don yă shari’anta mutanensa.
5“Ku tattara mini shafaffuna,
waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”
6Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa
gama Allah kansa alƙali ne. Sela

7“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana,
Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku.
Ni ne Allah, Allahnku.
8Ba na tsawata muku saboda hadayunku
ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.
9Ba na bukatan bijimi daga turkenku
ko awaki daga garkunanku,
10gama kowace dabbar kurmi nawa ne,
da kuma shanu a kan dubban tuddai.
11Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu
kuma halittun filaye nawa ne.
12Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba,
gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.
13Ina cin naman bijimai ne
ko ina shan jinin awaki ne?

14“Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,
ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,
15ku kira gare ni a ranar wahala;
zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

16Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina
ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?
17Kun ƙi umarnina
kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku
18Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi;
kukan haɗa kai da mazinata.
19Kuna amfani da bakunanku don mugunta
kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.
20Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku
ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.
21Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru;
kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne.
Amma zan tsawata muku
in kuma zarge ku a fuskarku.

22“Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah,
ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.
23Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni,
ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa
Ko kuwa gare shi kuma wanda ya lura da hanyarsa / zan nuna
ceton Allah.”
Copyright information for HauSRK