Psalms 52
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ▼▼Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” 1Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?Me ya sa kake fariya dukan yini,
kai da kake abin kunya a idanun Allah?
2Harshenka kan shirya hallaka;
yana nan kamar reza mai ci,
kana ta ruɗu.
3Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,
ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela
4Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,
Ya kai harshe mai ruɗu!
5Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.
Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;
zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela
6Masu adalci za su ga su ji tsoro;
za su yi masa dariya, suna cewa,
7“Yanzu, ga mutumin
da bai mai da Allah mafakarsa ba
amma ya dogara a yawan arzikinsa
ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
8Amma ni kamar itace zaitun ne
ina haɓaka a gidan Allah;
na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah
har abada abadin.
9Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;
a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.
Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.
Copyright information for
HauSRK