‏ Psalms 54

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil
Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.
ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?”

1Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka;
ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
2Ka ji addu’ata, ya Allah;
ka saurari maganar bakina.

3Baƙi suna kawo mini hari;
mutane marasa imani suna neman raina,
mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

4Tabbatacce Allah ne mai taimakona,
Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

5Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina;
cikin amincinka ka hallaka su.

6Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka;
zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
7Gama ya cece ni daga dukan wahalolina,
idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.
Copyright information for HauSRK