‏ Psalms 56

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam.
Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat.

1Ka yi mini jinƙai,
ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi;
dukan yini suna matsa harinsu.
2Masu ɓata sunana suna bina dukan yini;
da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

3Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
4Ga Allah wanda maganarsa nake yabo
ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

5Dukan yini sun yi ta juya maganata;
kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.
6Sun haɗa baki, sun ɓoye,
suna kallon takawata
suna a shirye su ɗauki raina.
7Sam, kada ka bari su kuɓuce;
cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.

8Ka lissafta makokina;
ka jera hawayena a littafinka,
Ko kuwa / ka sa hawayena a salkan ruwan inabinka

ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
9Ta haka abokan gābana za su juya da baya
sa’ad da na nemi taimako.
Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

10Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa,
ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,
11ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?

12Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah;
zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.
13Gama ka cece ni
Ko kuwa raina
daga mutuwa
da kuma ƙafafun daga tuntuɓe,
don in yi tafiya a gaban Allah
cikin hasken rai.
Ko kuwa a ƙasar masu rai

Copyright information for HauSRK