‏ Psalms 58

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.
Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.

1Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai?
Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?
2Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci,
da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.

3Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce;
daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.
4Dafinsu ya yi kamar dafin maciji,
kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,
5da ba ya jin muryar gardi,
kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.

6Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah;
ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!
7Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa;
sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.
8Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya,
kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.

9Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa,
ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.
Ma’anar Ibraniyancin wannan aya ba tabbatacce ba ne.

10Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu,
sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11Sa’an nan mutane za su ce,
“Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai;
tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”
Copyright information for HauSRK