Psalms 59
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. ▼▼Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. 1Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah;ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
2Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta
ka kuma cece ni daga masu kisa.
3Duba yadda suka kwanta suna jirana!
Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni
ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
4Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini.
Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
5Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Allah na Isra’ila,
ka tashi ka hukunta dukan al’ummai;
kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela
6Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
7Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu,
suna tofar da takuba daga leɓunansu,
suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya;
kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
9Ya ƙarfina, na dogara gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata, 10Allah mai ƙaunata.
Allah zai sha gabana
zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
11Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu,
in ba haka mutanena za su manta.
Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai,
ka kuma kawar da su.
12Saboda zunuban bakunansu,
saboda maganganun leɓunansu,
bari a kama su cikin fariyarsu.
Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
13ka cinye su da hasala,
ka cinye su sarai.
Sa’an nan za a sani a iyakar duniya
cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela
14Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
15Suna ta yawo neman abinci
su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
16Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
17Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata,
Allah mai ƙaunata.
Copyright information for
HauSRK