Psalms 7
Wani shiggayiyon ▼▼Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.
ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin. 1Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka;ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
2in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki
su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.
3Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure
aka kuwa sami laifi a hannuwana,
4in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni
ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,
5to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini;
bari yă tattake raina a ƙasa
ya sa in kwana a ƙura. Sela
6Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka;
ka tashi gāba da fushin abokan gābana.
Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.
7Bari taron mutane su taru kewaye da kai.
Ka yi mulki a bisansu daga bisa;
8bari Ubangiji mai shari’ar mutane.
Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina,
bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.
9Ya Allah mai adalci,
wanda yake binciken tunani da zukata,
ka kawo ƙarshen rikicin mugaye
ka kuma sa adalai su zauna lafiya.
10Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka,
wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.
11Allah alƙali ne mai adalci,
Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.
12In mutum bai tuba ba,
Allah zai wasa takobinsa;
zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.
13Ya shirya makamansa masu dafi;
ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.
14Wanda yake da cikin mugunta
ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.
15Wanda ya haƙa rami
yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.
16Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa;
fitinarsa takan sauka a kansa.
17Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa
zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
Copyright information for
HauSRK