‏ Psalms 71

1A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka;
kada ka taɓa sa in sha kunya.
2Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka;
ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.
3Ka zama dutsena da kagarata,
inda kullum zan je.
Ka ba da umarni a cece ni,
gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata.
4Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye,
da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.

5Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,
ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
6Daga haihuwa na dogara gare ka;
kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.
Kullayaumi zan yabe ka.
7Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,
amma kai ne katangata mai ƙarfi.
8Bakina ya cika da yabonka,
ina furta darajarka dukan yini.

9Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa;
kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.
10Gama abokan gābana suna magana a kaina;
waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare.
11Suna cewa, “Allah ya yashe shi;
mu fafare shi mu kama shi,
gama ba wanda zai kuɓutar da shi.”
12Kada ka yi nisa da ni, ya Allah;
zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
13Bari masu zagina su hallaka da kunya;
bari waɗanda suke so su cutar da ni
su sha ba’a da kuma kunya.

14Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya;
zan yabe ka sau da sau.

15Bakina zai ba da labarin adalcinka,
zai yi maganar cetonka dukan yini,
ko da yake ban san yawansa ba.
16Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.
17Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini
har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.
18Ko sa’ad da na tsufa da furfura,
kada ka yashe ni, ya Allah,
sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa,
ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

19Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah,
kai da ka yi manyan abubuwa.
Wane ne kamar ka, ya Allah?
20Ko da yake ka sa na ga wahaloli,
masu yawa da kuma masu ɗaci,
za ka sāke mayar mini da rai;
daga zurfafan duniya
za ka sāke tā da ni.
21Za ka ƙara girmana
ka sāke ta’azantar da ni.

22Zan yabe ka da garaya
saboda amincinka, ya Allah;
zan rera yabo gare ka da molo,
Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
23Leɓunana za su yi sowa don farin ciki
sa’ad da na rera yabo gare ka,
ni, wanda ka fansa.
24Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci
dukan yini,
gama waɗanda suka so su cutar da ni
sun sha kunya suka kuma rikice.
Copyright information for HauSRK