‏ Psalms 72

Ta Solomon.

1Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah,
ɗan sarki da adalcinka.
2Zai
Ko kuwa Bari yă; daidai da ayoyi 3-11 da kuma 17.
shari’anta mutanenka da adalci,
marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.

3Duwatsu za su kawo wadata ga mutane,
tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
4Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane
yă kuma cece’ya’yan masu bukata;
zai murƙushe masu danniya.
5Zai jimre muddin rana tana nan,
muddin akwai wata, har dukan zamanai.
6Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka,
kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
7A kwanakinsa adalai za su haɓaka
wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.

8Zai yi mulki daga teku zuwa teku
kuma daga Kogi
Wato, Yuferites
zuwa iyakar duniya.
Ko kuwa iyakar ƙasa

9Kabilun hamada za su rusuna a gabansa
abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa
za su ba da gandu gare shi;
sarakunan Sheba da Seba
za su ba shi kyautai.
11Dukan sarakuna za su rusuna masa
kuma dukan al’ummai za su bauta masa.

12Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka,
marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata
yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici,
gama jininsu yake a gabansa.

15Bari yă yi doguwar rayuwa!
Bari a ba shi zinariya daga Sheba.
Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa
su kuma albarkace shi dukan yini.
16Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar;
bari yă cika bisan tuddai.
Bari’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon;
bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
17Bari sunansa yă dawwama har abada;
bari yă ci gaba muddin rana tana nan.

Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa,
za su kuma ce da shi mai albarka.

18Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila,
wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
19Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada;
bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
Amin kuma Amin.

20Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.
Copyright information for HauSRK