Psalms 73
LITTAFI NA UKU
Zabura 73–89
Zabura ta Asaf. 1Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila,ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.
2Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi;
tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.
3Gama na yi kishin masu girman kai
sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.
4Ba sa yin wata fama;
jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.
5Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha;
ba su da damuwa irin na’yan adam.
6Saboda girman kai ya zama musu abin wuya;
tā da hankali ya zama musu riga.
7Daga mugayen zukatansu laifi kan fito
mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.
8Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa;
cikin girman kan suna barazana yin danniya.
9Bakunansu na cewa sama na su ne,
kuma harsunansu sun mallaki duniya.
10Saboda haka mutanensu sun juya gare su
suna kuma shan ruwa a yalwace. ▼
▼Ba a tabbatar da ma’anar Ibraniyancin da aka yi amfani da shi a wannan aya ba.
11Suna cewa, “Yaya Allah zai sani?
Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”
12Ga yadda mugaye suke,
kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
13Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta;
a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
14Dukan yini na sha annoba;
an hukunta ni kowace safiya.
15Da na ce, “Zan faɗa haka,”
da na bashe’ya’yanka.
16Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan,
sai ya zama danniya a gare ni
17sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah;
sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
18Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi;
ka jefar da su ga hallaka.
19Duba yadda suka hallaka farat ɗaya,
razana ta share su gaba ɗaya!
20Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka,
haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji,
za ka rena su kamar almarai.
21Sa’ad da zuciyata ta ɓaci
hankalina kuma ya tashi,
22na zama marar azanci da jahili;
na zama kamar dabba a gabanka.
23Duk da haka kullum ina tare da kai;
ka riƙe ni a hannun damana.
24Ka bishe ni da shawararka,
bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.
25Wa nake da shi a sama in ba kai ba?
Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.
26Jikina da zuciyata za su iya raunana,
amma Allah ne ƙarfin zuciyata
da kuma rabona har abada.
27Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka;
kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.
28Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah.
Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata;
zan yi shelar dukan ayyukanka.
Copyright information for
HauSRK