‏ Psalms 74

Maskil
Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.
na Asaf.

1Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah?
Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?
2Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa,
kabilar gādonka, wadda ka fansa,
Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.
3Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai,
dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.

4Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu;
suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.
5Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura
don yanka itatuwa a kurmi.
6Sun ragargaje dukan sassaƙar katako
da gatura da kuma gudumarsu.
7Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus;
suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.
8Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!”
Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.

9Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba;
ba sauran annabawan da suka ragu,
kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.
10Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah?
Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?
11Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama?
Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!

12Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa;
ka kawo ceto a kan duniya.

13Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka;
ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.
14Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa
ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.
15Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka;
ka busar da koguna masu ruwa.
16Yini naka ne, dare kuma naka ne;
ka kafa rana da wata.
17Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;
ka yi rani da damina.

18Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji,
yadda wawaye suka ɓata sunanka.
19Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji;
kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.
20Ka kula da alkawarinka,
domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.
21Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya;
bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.
22Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka;
ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.
23Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka,
ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.
Copyright information for HauSRK