Psalms 76
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. 1A cikin Yahuda an san Allah;sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
2Tentinsa yana a Salem
mazauninsa yana a Sihiyona.
3A can ya kakkarya kibiyoyin wuta,
garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela
4Darajarka tana da haske,
fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
5Jarumawa sun zube kamar ganima
sun yi barcinsu na ƙarshe;
ba ko jarumi guda
da zai iya ɗaga hannuwansa.
6A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub,
doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
7Kai kaɗai ne za a ji tsoro.
Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
8Daga sama ka yi shelar hukunci,
ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
9sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a,
don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela
10Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo,
waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
11Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su;
bari dukan ƙasashen maƙwabta
su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
12Ya kakkarya ƙarfin masu mulki;
sarakunan duniya suna tsoronsa.
Copyright information for
HauSRK