Psalms 77
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce. 1Na yi kuka ga Allah don taimako;na yi kuka ga Allah don yă ji ni.
2Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji;
da dare na miƙa hannuwa ba gajiya
raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.
3Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi;
na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela
4ka hana idanuna rufewa;
na damu ƙwarai har ba na iya magana.
5Na yi tunani kwanakin da suka wuce,
shekarun da suka wuce da daɗewa;
6na tuna da waƙoƙina da dare.
Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.
7“Ubangiji zai ƙi ne har abada?
Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?
8Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada?
Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?
9Allah ya manta yă yi jinƙai?
Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela
10Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan,
shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
11Zan tuna da ayyukan Ubangiji;
I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
12Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka
in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
13Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne.
Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?
14Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai;
ka nuna ikonka a cikin mutane.
15Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka,
zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela
16Ruwaye sun gan ka, ya Allah,
ruwaye sun gan ka suka firgita;
zurfafan gaske sun girgiza.
17Gizagizai sun sauko da ruwa,
sararin sama suka buga tsawa;
kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.
18Aka ji tsawanka a cikin guguwa,
walƙiyarka ta haskaka duniya;
duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.
19Hanyarka ta bi ta cikin teku,
hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye,
duk da haka ba a ga sawunka ba.
20Ka bi da mutanenka kamar garke
ta hannun Musa da Haruna.
Copyright information for
HauSRK