Psalms 81
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. ▼▼Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
Ta Asaf. 1Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
2Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,
ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
3Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata,
da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;
4wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila,
farilla ta Allah na Yaƙub.
5Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf
sa’ad da ya fito daga Masar.
Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.
6Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku;
an’yantar da hannuwansu daga kwando.
7Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku,
na amsa muku daga girgijen tsawa;
na gwada ku a ruwan Meriba. Sela
8“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku,
in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!
9Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku;
ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.
10Ni ne Ubangiji Allahnku
wanda ya fitar da ku daga Masar.
Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
11“Amma mutanena ba su saurare ni ba;
Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.
12Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare
don su bi dabararsu.
13“A ce mutanena za su saurare ni,
a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,
14da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu
in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!
15Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki,
hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.
16Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau;
da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”
Copyright information for
HauSRK