‏ Psalms 83

Waƙa ce. Zabura ta Asaf.

1Ya Allah, kada ka yi shiru;
kada ka tsaya cik,
ya Allah, kada ka daina motsi.
2Dubi yadda abokan gābanka suke fariya,
dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
3Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka;
suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.
4Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma,
don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”

5Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare;
suka haɗa kai gāba da kai,
6tentunan Edom da na mutanen Ishmayel,
na Mowab da kuma na Hagirawa,
7Gebal, Ammon da Amalek,
Filistiya, tare da mutanen Taya.
8Har Assuriya ma ta haɗa kai da su
don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Sela

9Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan,
yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,
10waɗanda suka hallaka a En Dor
suka zama kamar juji a ƙasa.
11Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib,
dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,
12waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki
wuraren kiwon Allah.”

13Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna,
kamar yayin da iska take hurawa,
14kamar yadda wuta ke cin kurmi
ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,
15haka za ka kore su da iska mai ƙarfi
ka kuma firgita su da guguwarka.
16Ka rushe fuskokinsu da kunya
don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.

17Bari su kasance cikin kunya da taƙaici;
bari su hallaka cikin wulaƙanci.
18Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji,
cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.
Copyright information for HauSRK