Psalms 85
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. 1Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji;ka mai da nasarorin Yaƙub.
2Ka gafarta laifin mutanenka
ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
3Ka kau da dukan fushinka
ka kuma juye daga hasalar fushinka.
4Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu,
ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
5Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne?
Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
6Ba za ka sāke raya mu ba,
don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
7Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji,
ka kuma ba mu cetonka.
8Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa;
ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa,
amma kada su koma ga wauta.
9Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa,
don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
10Ƙauna da aminci za su sadu;
adalci da salama za su yi wa juna sumba.
11Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa,
adalci kuma yă duba daga sama.
12 Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau,
ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
13Adalci na tafiya a gabansa
yana shirya hanya domin ƙafafunsa.
Copyright information for
HauSRK