Psalms 87
Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. 1Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona
fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.
3Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke
Ya birnin Allah, Sela
4“Zan lissafta Rahab
a cikin waɗanda suka san ni,
Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush,
zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”
5Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce,
“Wannan da wancan an haifa a cikinta,
Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”
6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa,
“An haifi wannan a Sihiyona.” Sela
7Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera,
“Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”
Copyright information for
HauSRK