‏ Psalms 88

Waƙa ce, Zabura ta’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannot
Kan magana, mai yiwuwa muryar “Tsananin Baƙin Ciki.”
maskil
Kan magana, mai yiwuwa kalma waƙa ce.
na Heman dangin Ezra.

1Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni,
dare da rana ina kuka a gabanka.
2Bari addu’ata ta zo a gabanka;
ka kasa kunne ga kukata.

3Gama raina yana cike da wahala
rayuwata tana gab da kabari.
Da Ibraniyanci Sheol

4An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami;
ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
5An ware ni tare da matattu,
kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari,
waɗanda ba ka ƙara tunawa,
waɗanda aka yanke daga taimakonka.

6Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa
cikin zurfafa mafi duhu.
7Hasalarka tana da nauyi a kaina;
ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela
8Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni
ka sa na zama abin ƙyama a gare su.
An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
9idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki.

Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana;
na tā da hannuwana zuwa gare ka.
10Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne?
Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela
11Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne,
ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
12An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne,
ko ayyukan adalcinka a lahira?

13Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;
da safe addu’ata kan zo gabanka.
14Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni
ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?

15Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu;
na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
16Hasalarka ta sha kaina;
razanarka ta hallaka ni.
17Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa;
sun mamaye ni ɗungum.
18Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;
duhu ne abokina na kurkusa.
Copyright information for HauSRK