Psalms 89
Maskil ▼▼ Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce.
na Etan dangin Ezra. 1Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada;da bakina zan sanar da amincinka
a dukan zamanai.
2Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada,
cewa ka kafa amincinka a sama kanta.
3Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena,
na rantse wa Dawuda bawana,
4cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada
in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela
5Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji,
amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
6Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji?
Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?
7Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro;
shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
8Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka?
Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
9Kana mulkin teku mai tumbatsa;
sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.
10Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe;
da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka.
11Sammai naka ne, haka kuma duniya;
ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
12Ka halicce arewa da kudu;
Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
13Hannunka mai iko ne;
hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.
14Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka;
ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.
15Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari
waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.
16Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini;
suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.
17Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu,
kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka. ▼
▼ƙaho a nan na kwatanta mai ƙarfi.
18Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce,
ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.
19Ka taɓa yin magana cikin wahayi,
ga mutanenka masu aminci ka ce,
“Na ba wa jarumi ƙarfi;
na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane.
20Na sami Dawuda bawana;
da mai na mai tsarki na shafe shi.
21Hannuna zai kasance tare da shi;
tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi.
22Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji;
babu mugun mutumin da zai danne shi.
23Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa
in kashe dukan abokan gābansa.
24Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi,
kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa.
25Zan sa hannunsa a bisa teku,
hannunsa na dama a bisa koguna.
26Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina,
Allahna, Dutse mai cetona.’
27Zan kuma naɗa shi ɗan farina,
mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.
28Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada,
alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.
29Zan kafa zuriyarsa har abada,
kursiyinsa muddin sammai suna nan.
30“In’ya’yansa maza suka yashe dokata
ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,
31in suka take ƙa’idodina
suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,
32zan hukunta zunubinsu da sanda,
laifinsu da bulala;
33amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba,
ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.
34Ba zan take alkawarina ba
ko in canja abin da leɓunana suka ambata.
35Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina,
ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,
36cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada
kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;
37zai kahu har abada kamar wata,
amintacciyar shaida a cikin sarari.” Sela
38Amma ka ƙi, ka yi ƙyama
ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka.
39Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka
ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura.
40Ka rurrushe dukan katangansa
ka sa kagaransa suka zama kufai.
41Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi;
ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa.
42Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa;
ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki.
43Ka juye bakin takobinsa
ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba.
44Ka kawo ƙarshen darajarsa
ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa.
45Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa;
ka rufe shi da mayafin kunya. Sela
46Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne?
Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
47Ka tuna yadda raina mai wucewa ne.
Gama ka halicce dukan mutane ba amfani!
48Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba,
ko yă cece kansa daga ikon kabari? Sela
49Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā,
wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?
50Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a,
yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai,
51zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji,
da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka.
52Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada!
Amin kuma Amin.
Copyright information for
HauSRK